News
Da ƴan Nijeriya sun san halin da wasu ƙasashen ke ciki da sun gode wa Allah – Buhari
Daga kabiru basiru fulatan
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce – da ‘yan ƙasar sun san irin halin matsi da takwarorinsu na ƙasashen Afirka ke ciki da sun gode wa Allah.
BBC ta rawaito cewa a wata sanarwa da mai taimaka wa shugaban kan kafofin yada labarai Malam Garba Shehu ya fitar, ya ce shugaban ya fadi hakan ne a yau Asabar lokacin da ya kai wa Sarkin Katsina Dr Abdulmumini Kabir Usman ziyara a fadarsa.
DA ƊUMI-ƊUMI: An kwantar da Osinbajo a asibiti
Ya kara da cewa ”Muna kira ga mutane da su yawaita haƙuri, muna iya bakin ƙoƙarinmu. Babu abin da ya fi zaman lafiya, muna roƙon Allah ya ba mu damar ganin bayan masu ƙoƙarin wargaza mana zaman lafiyar ƙasarmu.”
Shugaban ya ce zai ci gaba da yin bakin ƙoƙarinsa wajen yalwata wa ‘yan kasar bayan jin ƙorafe-ƙorafe kan halin da ‘yan ƙasar ke ciki daga bakunan gwamnan jihar Aminu Bello Masari da kuma Sarkin Katsina.
”Da mutanenmu sun san irin halin matsin rayuwa da wasu ƙasashen Afirka ke ciki a halin yanzu, da sun gode wa Allah game da halin da suke ciki a ƙasar nan,” in ji Shugaban na Najeriya.
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
