Connect with us

News

Mun fi samun tsaro lokacin Jonathan — Ƙungiyar ƴan Arewa By muhammad muhammad zahraddin December 30, 2021 0

Published

on

Jonathan ebele
Spread the love
Gamaiyar Ƙungiyoyi masu Zaman Kansu a Arewa, a ƙarƙashin inuwar CNG, sun koka kan yawaitar garkuwa da mutane, kashe-kashe da rashin tsaro a ƙasar nan.
Daraktan sadarwa na CNG, Ismail Musa ya ce Shugaba Muhammadu Buhari ya dawo da Nijeriya kamar lokacin tsohon shugaban ƙasa Jonathan Goodluck, lokacin da rashin tsaron bai yi ƙamari ba kamar yanzu.
A wani shirin tattaunawa na jaridar Vanguard a jiya Laraba, Musa ya caccaki Buhari kan yadda ya gaza daƙile rashin tsaro a ƙasa.
“Mu yanzu abin da mu ke roƙon su shine, ka san rayuwar ɗan adam na da daraja, ita ce ma ƙashin baya.
“Mu in ma za ka yi wani abu, to ka maida mu baya lokacin da ka samu yanayin rashin tsaro, ka ga za mu iya cewa mun hakura da hakan saboda kamar yadda kididdiga ta nuna, kowa ya san dai ba kamar yanzu ba.
“To gaskiya, mun shiga uku a ce irin waɗannan mutanen ne su ke mulkar mu,” in ji shi.
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *