News
Yajin aikin Adaidaita: ‘Yan sanda sun kama mutum 40 – DSP Kiayawa
Daga Usman Abdullah jibirin
Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta kama kimanin mutum 40 bisa zargin afka wa wasu masu sana’ar babur mai kafa uku, saboda kin shiga yajin aikin da su ke yi, tare da yi wa masu tafiya a kafa kwace.
Mai magana da yawun rundunar a Kano, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana hakan ga manema labarai a ranar Lititin.
A cewar SP Abdullahi Haruna Kiyawa, mutanen da suka kama suna dauke da makamai inda suke tare hanya suna yi wa mutane kwace da tilasta wa masu kananan motoci daukar kaya sauke mutanen da suka dauko don rage musu hanya.
Tun a safiyar yau Litinin a ka girke jami’an tsaro na ‘yan sanda da na rundunar tsaro ta civil Defense wasu daga cikin manyan titunan Kano, domin jiran ko ta kwana na yiwuwar samun rikici a lokacin da masu babur mai kafa uku a jihar suka fara yajin