News
El-Rufa’i ya baiwa Buhari shawarar ƙara farashin man fetur zuwa naira 302
Daga kabiru basiru fulatan
Wataƙila gwamnatin Najeriya ta kara farashin man fetur zuwa naira 302 a kan kowa ce lita a wata mai zuwa, Fabrairu, kamar yadda majalisar kasa kan tattalin arziki ta bayar da shawara a watan Nuwamba na 2021, in ji jaridar TheCable.
Jaridar ta ruwaito cewa tana ganin wannan na daga cikin shirin gwamnati na janye hannunta kacokan daga harkar sanya farashin man, domin kawo karshen tallafin da take biya a kowane wata, ta yadda kasuwa za ta yi halinta a samu gogayya kan farashin.
A yanzu dai ana sayar da man fetur a yawancin sassan Najeriya a tsakanin naira 162 da 165 a kan kowace lita.
Kwamitin wucin-gadi na majalisar kula da tattalin arziki wanda ya tattauna da kamfanin mai na kasar (NNPC) a kan farashin da ya dace a sa shi ne ya bayar da shawarar kara kudin ta hanyar janye tallafin.
Gwamnan jihar Kaduna Mallam Nasir El-Rufai, wanda shi ne shugaban kwamitin, shi ya gabatar da rahoton.