Connect with us

Sports

Kasuwar ƴan ƙwallo: Makomar Aubamayeng, Muller, Haaland, Guimaraes, Burn, Traore

Published

on

Spread the love

Daga muhammad muhammad zahraddin

Dan wasan gaban Bayern Munich da Jamus Thomas Muller ya ja hankalin Newcastle United da Everton, yayin da kwantiraginsa ke cikin shekara ta karshe da kungiyar ta Bundesliga. (Sportbild)

Barcelona na aiki kan wani shiri na tara Yuro miliyan 100 (£83.5m) don daukar nauyin sayen dan wasan Borussia Dortmund da Norway Erling Haaland mai shekara 21 a bazara. (Goal)

Advertisement

Dan wasan tsakiya na Lyon Bruno Guimaraes ya shaida wa kulob din cewa yana son komawa Newcastle, wacce ta gabatar da tayin dan wasan na Brazil mai shekara 24. (L’Equipe)

Brighton ta ki amincewa da tayin da Newcastle ta yi mata na dan wasan bayan Ingila Dan Burn, mai shekara 29. (Athletic)

Frank Lampard ne kan gaba a cikin masu neman zama kocin Everton. (Indepenet)

Advertisement

Newcastle ta koma tattaunawa don siyan dan wasan baya dan kasar Holland Mitchel Bakker daga Bayer Leverkusen, inda kungiyar ta Bundesliga ke son siyar da dan wasan mai shekaru 21 ga Magpies a cikin watan Janairu. (90mints)

Tottenham ta amince ta bada aron dan wasan tsakiyar Faransa Tanguy Ndombele, mai shekara 25, ga Valencia. (Telefoot)

Dan wasan Wolves dan kasar Sipaniya – da Tottenham ke nema – Adama Traore, mai shekara 26, shi ma yanzu ana kallonsa a matsayin zabi ga Barcelona idan har za ta iya samun yarjejeniyar fitar da dan wasan gaban Faransa Ousmane Dembele, mai shekara 24, daga kungiyar. (ESPN)

Advertisement

Liverpool ta tuntubi dan wasan Juventus da Argentina Paulo Dybala, wanda kwantiraginsa zai kare a bazara. (TuttoMercato – ta Sun)

Fatan Arsenal na sayen dan wasan tsakiya na Brazil Arthur Melo, mai shekara 25, a matsayin aro har zuwa karshen kakar wasa ta bana daga Juventus na cikin shakku. (Sports)

Ana sa ran Arsenal za ta dage wajen zawarcin dan wasan Aston Villa dan kasar Brazil Douglas Luiz, mai shekara 23, kafin karshen kasuwar musayar ‘yan wasa ta bana. (Birmingham Mail)

Advertisement

West Ham da Crystal Palace na sa ran zawarcin dan wasan gaban Senegal da Marseille Bamba Dieng, mai shekara 21 (RMC Sport)

AC Milan ta mika tayin dan wasan gaban Arsenal Pierre-Emerick Aubameyang amma dan kasar ta Gabon mai shekara 32, ya bukaci fiye da ninki biyun kudin da Zlatan Ibrahimovic ke karba a kulob din Italiya. (Star)

Manchester City na shirin dauko dan wasan gaban kasar Hungary Zalan Vancsa mai shekaru 17 daga MTK Budapest. (Telegraph)

Advertisement

Brighton ta ga bukatar da Braga ta yi watsi da tayin da take yi na neman dan wasan Spain Abel Ruiz, mai shekara 21. (minti 90)

Dan wasan bayan Faransa William Saliba, mai shekara 20, yana son komawa Arsenal daga aronsa da Marseille a bazara, duk da jita-jitar da ke nuna cewa zai iya komawa kulob din Ligue 1 a kan yarjejeniyar dindindin. (ball.london)

Tottenham na iya amfani da dan wasan tsakiya na Argentina Giovani Lo Celso a wani bangare na cinikin dan wasan baya na Brazil da Newcastle ke zawarci Diego Carlos, mai shekara 28, daga Sevilla. (Sun)

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *