News
2023: Zan Fito Takarar Shugaban Kasa – Bokola Saraki

Daga Muhammad Muhammad zahraddini
Tsohon shugaban Majalisar Dattijan Nigeriya Bukola Saraki ya nuna Sha’awar sa ta tsayawa takarar shugabancin kasa a shekarar 2023.
Furucin nasa ya biyo bayan shugaban jam’iyyar APC na kasa Bola Ahmad Tinubu, gwamnan Jahar Ebonyi Dave Umahi, Sanata Chip Whip Orji Kalu da kuma tsohon gwamnan Jahar imo Rochas Okoracha da suka nuna makamanciyar sha’awa kan takarar.
Tsohon gwamnan Jahar kwara Yace yana da karfin tarihin da gogewa akan gabatar da tsauraran matakai.
An haifi Bukola Saraki 19 ga watan Disamba 1962 kuma da ne ga sanatan jamhuriyya ta biyu marigayi Olusola Saraki.
Ya fada a shafin sa na Facebook yace: “Ba jimawa na mayar wa wani mabiyi na a Twitter da yake kaunar dubun ku yake bukatar hadin kai domin ceto Nigeriya.