News
Kotun Kano ta yanke wa mace hukuncin share unguwarsu kan kiran maƙociyarta karuwa

Daga muhammad muhammad zahraddin
Wata mata mai suna Rabi a birnin Kano ta fara aiwatar da hukuncin da alƙalin Kotun Shari’ar Musulunci ya yanke mata sakamakon kama ta da laifin yi wa maƙociyarta ƙazafin “karuwanci”.
Mai Shari’a Halhalatul Khuza’i ne ya kama Rabi mazauniyar Rijiyar Zaki da laifin sannan ya yanke mata hukuncin share titin unguwarsu baki ɗaya na tsawon kwana 30.
Malama Rabi ta ce ba ta da wani ƙorafi game da hiukuncin, tana mai cewa ta ji daɗi da hukuncin bai wuce hakan ba.