Entertainment
Ƴar Atiku Abubakar, Nana, ta baiwa jarumin Nollywood kyautar fili a Abuja

Daga kabiru basiru fulatan
Nana Atiku, ƴar tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ta baiwa wani jarumin masana’antar fina-finai ta kudancin Nijeriya, Nollywood, Zubby Michael kyautar fili a Abuja domin taya shi murnar cikar shekara 37 da haihuwa.
Zubby ya wallafa hotunan sa da Nana a shafinsa na instagram, inda ya baiyana cewa ta bashi kyautar filin.
Ya wallafa cewa “kyautar tunawa da ranar haihuwa mafi girma.”
Jarumin ya godewa Nana, wacce mai harkokin filaye da gidaje ce a Abuja, in da ya ce “Nagode Allah Ya yi albarka.”
Ita ma Nana ɗin ta wallafa hotunan ta da jarumin inda ta taya shi murnar zagayowar ranar haihuwar sa.
“Ina taya jarumin da ya fi kayatar da ni. Namiji mai zuciyar gwal. Ba zan dena samun farin ciki da ga gare ka ba. Allah Ya ci gaba da buɗa maka kamar yadda ka ke taimakon wasu. Kullum ina mai alfahari da kai. Ina taya ka murnar zagayowar ranar haihuwar ka. Allah Ya sanyawa rayuwar ka albarka,” in ji Nana.