Connect with us

Entertainment

Fagen Nishadi: Duk fim din da nayi ana biyana daga dubu 2 zuwa dubu 5 kacal — Ladi Cima.

Published

on

Spread the love

Daga yasir sani abdullahi

 

 

Advertisement

Daga Bakin Mai Ita wani shiri ne na BBC Hausa da ke kawo muku hira da fitattun mutane kan wasu abubuwan da suka shafi rayuwarsu zalla.

A wannan kashi na 85 din, shirin ya tattauna da fitacciyar ƴar wasan Hausa, wadda ke fitowa a matsayin uwa ko kuma kaka a masana’antar Kannywood wato Ladin Cima Haruna wadda aka fi sani da Tambaya.

Ta bayyana cewa ta soma harkar fim bayan rasuwar mijinta inda ta ce dama tun a baya tana da sha’awar fim din. Ta ce Kaduna suke zuwa su yi fim saboda a zamanin babu gidan talabijin a Kano.

Advertisement

Ta bayyana cewa ta soma fim tun zamanin mulkin tsohon shugaban Najeriya Yakubu Gowon.

Ta bayyana cewa ta yi aiki a asibiti kuma zamanin Kabiru Gaya na gwamnan Kano ne ya ɗauke su aikin asibiti amma a yanzu ta yi ritaya.

A cewarta, a tsawon lokacin da ta ɗauka tana fim, ba ta yi fim din da za a ɗauko dubu ashirin ko talatin ko hamsin a bata ba inda ta ce ana biyanta daga dubu biyu zuwa dubu biyar idan ta yi fim.

Advertisement

Ta ce a zamanin, ba a biyansu kuɗi, amma saboda sha’awar fim ɗin, suna ƙagara ranar Juma’a ta zo su tafi yin fim ɗin idan sun kammala sai Lahadi su koma

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *