Connect with us

News

Sojoji sun hallaka ƴan ta’adda 120, yayin da 965 su ka sallata

Published

on

FB IMG 16445052057925694
Spread the love

Daga kabiru basiru fulatan

 

 

Advertisement

Shelkwatar Tsaro ta Ƙasa ta baiyana cewa jami’an rundunar soji ta Operation Hadin Kai sun hallaka ƴan Boko Haram da ISWAP sama da 120 a Arewa-maso-Gabas a makonni uku da su ka gabata.

Darakatan Yaɗa Labarai na Rundunar Soji, Bernard Onyeuko ne ya baiyana hakan a yau Alhamis, yayin da ya ke bada bayanai a kan aikace-aikacen sojin Nijeriya da ga 10 ga watan Janairu zuwa 20 ga Febrairu.

Onyeuko ya ce ƴan ISWAP da dama, da su ka haɗa da Amiran su da aka sojojin hayar su ƴan ƙasashen waje da su ke haɗa musu ababan fashewa, duk sun mutu a yayin luguden wuta ta sama da ƙasa da sojoji ke yi.

Advertisement

A cewar sa, a wannan lokacin, ƴan ta”adda 965 da iyalan su ne su ka miƙa kan su ga jami’an tsaro a turare daban-daban a yankin.

Onyeuko ya ƙara da cewa yan ta’adda 104 da ga cikin su ƴan ƙungiyar ISWAP ne, in da ya ce an tserar da mutane 25 da a ka yi garkuwa da su.

A cewar sa, an dauki bayanan yan ta’addan da su ka sallata sannan a ka miƙa su ga hukumomin da su ka dace domin ɗaukar mataki na gaba.

Advertisement

Ya kuma ƙara da cewa sojojin sun samu gagarumar nasara a gurare da dama a Adamawa da Yobe a yankin Goniri a Ƙaramar Hukumar Gujba da ke Yobe.

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *