Connect with us

Entertainment

Ba a Saka wasu matan a Film sai anyi lalata da su, Maganar bayarda 2K gaskiya ne – Sarkin waka

Published

on

FB IMG 16445586650005269
Spread the love

Daga kabiru basiru fulatan

 

 

Advertisement

Naziru M Ahmad, wanda aka fi sani da Sarkin Waka, ya bayyana hakan ne a cikin wani faifan bidiyo, jim kadan bayan Ali Nuhu da Falalu A Dorayi sunyi wa Hajiya Ladin Cimma Haruna Martani kan kudin da ake ba ta a fim.

Yace Abun da dattijuwar can ta fada gaskiya ne…. Dubu biyu dubu ukku Ake bawa dattawa Yan film.

Sannan yace ya Rantse da Allah Haka Akeyi Idan kuma Akwai Wanda ya Isa yazo ya Musu to Yana jira

Advertisement

Sarkin Waka ya ce ana cin zarafin wasu daga cikin mata ta hanyar lalata da su saboda za a sanya su a fim, wayansu kuma a kyauta hasali ma sune zasu biya kudi a sanya su.

Ya ce masana’antar tana samun nakasu, kuma ya kalubalanci duk wayanda suka karyata zancen hajiyar da cewar su yi rantsuwa kan abunda da ta fada ba gaskiya ba ne, inji rahoton Daily True Hausa

Naziru ya kalubalanci ali nuhu da Falalu A Dorayi bisa take gaskiya kan furucin su, ya ce zasu iya musa masa kan kalaman da ya fada idon karya ne ba’a aikatawa.

Advertisement

 

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *