Sports
Kasuwar ƴan ƙallo: Madrid na son Tierney, Rangnick ya ƙular da ƴan wasan United, Barca na zawarcin Isak

- Daga kabiru basiru fulatan
Mauricio Pochettino na son Manchester United ta sayi kyaftin din Ingila Harry Kane, mai shekara 28, daga Tottenham, idan ya bar Paris St-Germain ya zama kocin kungiyar. (Telegraph)
Real Madrid ta saka dan wasan baya na Arsenal dan kasar Scotland Kieran Tierney mai shekaru 24 a jerin wadanda take zawarcin a bazara. (El Espanol – in Spanish)
‘Yan wasan Manchester United na jin takaicin yadda kociyan rikon kwarya Ralf Rangnick ke yi atisayen da suka yi imani da cewa “tsoho yayi ne”. (ESPN)
Aston Villa da Tottenham na cikin kungiyoyi hudu da ke son dauko dan wasan tsakiya na Chile Arturo Vidal mai shekaru 34 daga Inter Milan. (Calciomercato)
West Ham ta fara tattaunawa da dan wasan tsakiyar Jamhuriyar Czech, Tomas Soucek, mai shekara 26, kan sabon kwantaragi a London. (Insider Football)
Barcelona na son siyan sabon mai tsaron gida a wannan bazarar, (Mundo Deportivo – in Spanish)
Tottenham za ta iya doke Barcelona wajen siyan dan wasan AC Milan dan kasar Ivory Coast Franck Kessie mai shekaru 25. (Spots)
Barcelona na zawarcin dan wasan gaban Real Sociedad da Sweden Alexander Isak, mai shekara 22, wanda Arsenal ke zawarcinsa. (Sports)