Connect with us

Opinion

Aduk loƙacin da aka kusa kai ƙarshen wani zango na mulkin siyasa zakaga masu zawarcin kujerun madafun iko sunyi caa kowa yana gwada sa’arsa.

Published

on

IMG 20220113 WA0033
Spread the love

Daga kabiru basiru fulatan

A irin wannan yanayi yana da kyau masu zabe su rika kula da idon basira domin gudun faɗawa hannun mayaudara.

Advertisement

Domin mafi yawan masu neman mulkin siyasa suna yaudarar mutane da abun da mutanen suke so ne, ko kuma abun da mutanen suke fatan rabuwa dashi na wata musiba ko annoba, taɓangaren tsaro ne ko ta ɓangaren wasu cututtukan da suka zamewa al-ummar ƙasa, jiha, lardi ko gunduma alaƙaƙai.

Rimi-rimi dan takarar siyasa zai zo yatara talakawa yayi musu romon baka, labaran kanzon kurege da alkawarorin ƙarya wadanda shi kansa yasan ba zai iya cika su ba, amma tunda yanason wannan kujerar da yake hari, hakan ne hanya mafi sauƙi da zai sa mutane su yarda dashi.

Su kuma talakawa za su dauki kaunar duniya su dora masa domin aganinsu wannan alkawuran da yayi musu abune me yiyuwa a wajensa, hakan ne zai sa suyi kokari matuka domin ganin sun tura motarsa domin cikar burinsu na alƙawuran da yai musu, bayan motar ta tashi ba abin dazai saka musu dashi sai dai ya bule su da baƙin hayaƙi wanda zai hanasu ganin gaba ko baya.

Mulkin dimukuradiyya shine yabaiwa kowanne dan takara damar bayyana manufofinsa da kudurinsa domin wanda za’a mulka su tantance wanda suka yarda da manufofinsa da ƙudirinsa domin ya jagorancesu.

Advertisement

Sai dai mafi yawan ‘yan siyasa suna yin amfani da wannan damar ce domin boye mugun nufinsu na wawushe kudin talakawa da canjawa kudin talakawa wuri daga lalitar bitalmalin ‘yan kasa zuwa aljihunansu da na ‘ya’yansu.
A irin wannan yanayi yana da kyau masu zabe su rika kula da idon basira domin gudun faɗawa hannun mayaudara.

Domin mafi yawan masu neman mulkin siyasa suna yaudarar mutane da abun da mutanen suke so ne, ko kuma abun da mutanen suke fatan rabuwa dashi na wata musiba ko annoba, taɓangaren tsaro ne ko ta ɓangaren wasu cututtukan da suka zamewa al-ummar ƙasa, jiha, lardi ko gunduma alaƙaƙai.

Rimi-rimi dan takarar siyasa zai zo yatara talakawa yayi musu romon baka, labaran kanzon kurege da alkawarorin ƙarya wadanda shi kansa yasan ba zai iya cika su ba, amma tunda yanason wannan kujerar da yake hari, hakan ne hanya mafi sauƙi da zai sa mutane su yarda dashi.

Su kuma talakawa za su dauki kaunar duniya su dora masa domin aganinsu wannan alkawuran da yayi musu abune me yiyuwa a wajensa, hakan ne zai sa suyi kokari matuka domin ganin sun tura motarsa domin cikar burinsu na alƙawuran da yai musu, bayan motar ta tashi ba abin dazai saka musu dashi sai dai ya bule su da baƙin hayaƙi wanda zai hanasu ganin gaba ko baya.

Advertisement

Mulkin dimukuradiyya shine yabaiwa kowanne dan takara damar bayyana manufofinsa da kudurinsa domin wanda za’a mulka su tantance wanda suka yarda da manufofinsa da ƙudirinsa domin ya jagorancesu.

Sai dai mafi yawan ‘yan siyasa suna yin amfani da wannan damar ce domin boye mugun nufinsu na wawushe kudin talakawa da canjawa kudin talakawa wuri daga lalitar bitalmalin ‘yan kasa zuwa aljihunansu da na ‘y

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *