News
ASSU: Malamin jami’oi sun bayyana cewa tuni suka fidda kauna da gwamnatin Shugaba Buhari.
Daga Muhammad Muhammad zahraddin
Majalisar zartaswar kungiyar malaman jami’o’in Najeriya ASUU za ta fara zaman kwanaki biyu a jami’ar Legas, Akoka ranar Asabar domin yanke shawara kan maganar yajin aikin sai baba ta gani.
ASUU za ta gudanar da zabe ne kan wannan shawara kuma a sanarwa al’umma ranar Lahadi, wani mamba majalisa ya bayyana jaridar Punch.
Yace
“Ba shugaban kungiyarmu zai yanke shawara kan yajin aikinmu ba. Haka zalika ba wani dan majalisar zartaswa ne zai yanke shawara shi kadai ba. Za’a tattauna lamuran ne a zaman gana.”
“Sannan sai a gudanar da zabe. Abinda muka yanke shawara ranar Lahadi shi za’a yi.”
Kungiyar ASUU a ranar Juma’a ta bayyana cewa zata shiga yajin aiki saboda gwamnatn Buhari bata shirya cika alkawuran da tayi mata ba. ASUU ta siffanta abinda Gwamnatin tarayya ke yi matsayin abin kunya musamman kan na’urar IPPIS duk da hujjoji daga ofishin Odito-Janar cewa ba tada inganci.
A jawabin da ASUU ta saki ranar Juma’a, ta bayyana yadda Gwamnati ta ki aiwatar da shawarin da aka yanke a zaman ganawa daban-daban don inganta Ilimi a Najeriya. Shugaban kungiyar ASUU, shiyar jami’ar Jos, Dr Lazarus Maigoro, ya rattafa hannu kan jawabin.