News
Jiragen yaƙin Sojin Nijeriya sun hallaka Buba-Danfulani da sauran kwamandojin ISWAP a Tumbuns da Sambisa

Daga yasir sani abdullahi
An kashe Amir Buba Danfulani da wasu fitattun kwamandojin ISWAP hudu a Tumbuns da gatari a yankin Sambisa da ke Arewa-maso-Gabas a harin da sojojin Najeriya suka kai musu ta jiragen yaƙi.
PRNigeria ta jiyo cewa Danfulani, babban kwamandan ISWAP ne da ke da alhakin cusawa Fulani makiyaya aƙidar shiga ƙungiyar ta’addancin.
Hakazalika shi ne kuma da alhakin haɗa ayyukan ‘yan ta’addan, tun daga tura ‘yan keƙen asiri da kuma masu karɓar haraji.
Rundunar sojin saman Najeriya NAF ce ta gudanar da wannan sumame ta sama, ƙarƙashin rundunar ‘Operation Haɗin Kai’ a cikin mako ɗaya a wurare daban-daban.
Wata majiyar sirri ta shaidawa PRNigeria cewa, an tura Super Tucano, jirage masu saukar ungulu da sauran jiragen yaƙi a cikin ayyukan na tsawon mako guda da aka gudanar a lokaci guda a wurare daban-daban.
“Kafin aiwatar da wannan hari na musamman, bayanan sirri sun gano sansanonin horar da ‘yan ta’adda a Tumbun Kaiyowa da Tumbun Allura wadanda suka fi kai hare-haren ISWAP/Boko Haram.
Hakazalika ‘yan ta’addan su na amfani da sansanonin wajen harba makami mai linzami kan sansanin sojojin Najeriya da ke Mallam Fatori.
“Saboda haka, Rundunar Sojan Sama ta Operation Hadin Kai ta tura wasu jiragen da suka rage karfin ‘yan tada kayar baya domin hana kai hare-hare a nan gaba kan sojoji da wuraren abokantaka tare da tabbatar da nasarar ayyukan da ake yi.
“Jirgin ya jefa bama-bamai da dama a kan TUMBUN KAIYOWA da rokoki da igwa a TUMBUN ALLURA. An kuma hallaka ‘yan ta’addan da suka tsere da jirage masu saukar ungulu na yaki.
“An gudanar da makamancin haka a Parisu da Njimia da ke cikin dajin Sambisa, inda jiragen sama daban-daban guda uku suka yi ta kai hare-hare.
“Kawar da wadannan jiga-jigan ‘yan ta’adda, ko shakka babu zai aike da sako mai karfi ga ‘yan ta’addan da ke addabar yankin Arewa-maso-Gabas. A maimakon haka ana alakanta hakan ne da samun ƙwarin-gwiwa da sojojin Nijeriya da sauran jami’an tsaro su ka kawo wajen daƙile ayyukan ta’addanci.
PRNigeria ta jiyo da ga majiyoyin leken asirin cikin gida cewa an kashe wasu jiga-jigan ‘yan ta’adda biyar a harin jiragen yaƙi, waɗanda su ka haɗa da Musa Amir Jaish, Mahd Maluma, Abu-Ubaida, Abu-Hamza da Abu-Nura Umarun Leni.