Connect with us

News

Zaben 2023: Rabiu Musa Kwankwaso ya ƙaddamar da sabuwar ƙungiyar siyasa

Published

on

FB IMG 1645533133886
Spread the love

Daga kabiru basiru fulatan

 

Tsohon gwamnan jihar Kano da ke arewacin Najeriya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, yana jagorantar wani gagarumin taro na wasu manyan siyasar kasar karkashin wata kungiya mai suna The National Movement TNM.

Fitattun mutane da ƴan siyasa da suka halarci taron sun haɗa da Alhaji Tanko Yakasai da Capt Idris Wada, tsohon gwamnan Kogi da Rufai Alkali da Aminu Ibrahim Ringim, tsohon dan takarar gwamna a jihar Jigawa da kuma Inijiniya Buba Galadima.

Advertisement

Ana gudanar da taro ne a International Conference Centre da ke Abuja, babban birnin tarayyar kasar.

A jawabin Kwankwaso, ya ce wasu ƴan Najeriya ne da suka damu da abin da ke faruwar a ƙasar suka haɗa kai don ceto ta daga mawuyacin halin da ta shiga.Ya ce yunƙuri ne na ƴan Najeriya masu kishi da suke zaune a gida da kasashen waje.

A cewar Kwankwaso za su duƙufa wajen farfaɗo da tattalin arzikin kasar da inganta rayuwar ƴan kasa a birni da karkara

Advertisement

Ya ce sun shirya tsaf domin tunkarar matsalar tsaro da ta addabi Najeriya.

Kwankwaso ya ce za su yi wa makiyaya gata na ganin cewa ba a cinye musu burtalai ba, sannan za su bai wa manoma dukkan kariyar da suke bukata.

Tsohon gwamnan na jihar Kano, wanda dan jam’iyyar PDP ne, bai bayyana mukamin da yake son nema ba a wannan sabuwar kungiya ta siyasa.

Advertisement

Sai dai ana rade radin cewa zai fita daga jam’iyyar PDP sakamakon rashin jin dadin abubuwan da ke faruwa a cikinta. Kodayake bai tabbatar da hakan ba.

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *