Daga yasir sani abdullahi
News
Masu kutse na buƙatar $20,000 bayan garkuwa da shafukan intanet 34 na Mozambique

Wasu da ake zargin masu kutse ta intanet ne sun ƙwace iko da shafuka 34 na ƙasar Mozambique sa’o’i bayan gwamnatin ƙasar ta ce ta daƙile irin wannan harin a ranar Litinin.
Wata ƙungiya da ake kira “Yemeni Hackers” ta bayyana cewa ita ce ta yi kutsen.
Wasu daga cikin shafukan intanet da aka yi wa kutse sun haɗa da na hukumar kiyaye afkuwar bala’i da ma’aikatar hanyoyi da ta ruwa da ma’aikatar tsaro.
Masu kutsen sun ajiye saƙo a ɗaya daga cikin shafukan da suka yi wa kutsen inda suke buƙatar a biya su kuɗin fansa cikin sa’o’i 24 kafin su saki shafin.
Suna buƙatar a biya su dala dubu 20 ta hanyar bitcoin idan ba haka ba sun ce za su wallafa bayanan sirri na ƙasar.