News
‘Batira ne suka kama da wuta a ma’aikatar kuɗi’
Advertisements

Daga Muhammad Muhammad zahraddin
Gobara ta tashi a hedikwatar ma’aikatar kuɗi ta Najeriya da ke Abuja babban birnin ƙasar.
Advertisements
Advertisements
Babu tabbaci kan ko me ya jawo gobarar sai dai tuni ma’aikatan kashe gobara suka isa wurin.
Advertisements
Jaridar Punch a Najeriya ta ruwaito mai magana da yawun hukumar kashe gobara wato Abraham Paul inda ya ce ma’aikatansu na can suna ƙoƙarin kashe wutar.
Advertisements
Advertisements
A wani saƙo da ma’aikatar kuɗi da kasafi ta Najeriya ta wallafa a shafinta na Twitter, ta ce gobarar ba ta yi muni ba kamar yadda aka yi ta zuzutawa a shafukan sada zumunta inda ta ce wasu batira ne da aka keɓe suka kama da wuta a wani zaure da ke ƙasa a cikin hedikwatar ma’aikatar.
Advertisements
