Entertainment
Hotuna na da Aisha Humaira ba na aure ba ne, na talla ne — Mai-shadda
Daga kabiru basiru fulatan
Fitaccen Mai tsara fina-finan Hausa na Kannywood, Abba Bashir, wanda a ka fi sani da Mai-shadda ya musanta rahotannin da ke yawo a kafafen sadarwa cewa zai auri jaruma Aisha Ahmad, wacce a ka fi sani da Aisha Humaira.
A yau Alhamis ne dai Jaridar indaranka ta rawaito cewa Mai-shadda na daf da angwance wa da Aisha Humaira, bayan da ya wallafa hotunan da su ka ɗauka tare a shafinsa na Instagram.
“Zan yi wuff da gishiri ambassador.”, haka Mai-shadda ya rubuta a saman hotunan da ya wallafa a Instagram ɗin.
Bayan wallafar da ya yi, jaruma Aishat Humaira ta sake wallafa hotunan a shafinta na Instagram, inda ta haɗa da alamar soyaiya.
Hakan ne ya sanya a ka dinga yayata wa cewa aure jaruman na Kannywood za su yi.
Sai dai kuma wata majiya da ke kusa da Mai-shadda, a yammacin Alhamis ta shaida wa Daily Nigerian Hausa cewa hotunan ba na aure ba ne, na talla ne.
A cewar majiyar, jaruman biyu sun ɗauki hotunan ne domin yi wa Kamfanin Shehu Danƙwarai da ke kasuwar Kantin Kwari.
Majiyar ta ce nan ba da daɗewa ba Mai-shadda zai wallafa tallan a shafinsa na Instagram.
“in an jima kaɗan ma zai saki tallan a kan Instagram ɗin shi sabo da mutane su na ta damun shi da waya.
“Tallan Kamfanin Shehu Danƙwarai ne, in an jima zai sanya shi a Instagram,” in ji majiyar.