Connect with us

News

Dokar zaɓe: Buhari na son a goge sashen da ya ce masu muƙaman siyasa su sauka kafin zaɓe

Published

on

FB IMG 1645852717762
Spread the love

Daga kabiru basiru fulatan

 

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya buƙaci Majalisun Dokokin ƙasar su goge sashen da ya hana masu muƙaman siyasa neman takara a cikin sabuwar dokar zaɓen da ya sanya wa hannu a yau Juma’a.

Shugaban ya bayyana hakan ne yayin da yake sanya wa dokar hannu a fadarsa da ke Abuja.

Sashe na 84 (12) na Dokar Zaɓe ta 2022 ya buƙaci duk wani mai muƙamin siyasa ya ajiye muƙaminsa kafin ya tsaya wata takara a babban zaɓe.

Advertisement

Hakan na nufin za a tilasta wa wasu manyan ƙusoshin gwamnatin ta Buhari su sauka daga muƙamansu kafin babban zaɓe na 2023.

Buhari ya ce wasu daga cikin tanadin dokar za su haɓaka harkokin zaɓe “kamar 3, 9(2), 34, 41, 47, 84(9), (10), (11) da sauransu”.

“Sai dai abin ba haka yake ba… a sashe na 84 (12) wanda ya shatale masu riƙe da muƙaman siyasa game da zaɓensu da kuma jefa musu ƙuri’a a manyan tarukan jam’iyyu idan ba a gudanar da zaɓen ba cikin kwana 30 kafin zaɓe,” in ji shugaban.

Advertisement

Buhari ya shafe kusan kwana 25 kafin ya sanya wa dokar hannu, wadda ‘yan majalisar suka yi wa kwaskwarima sau biyu kafin ya amince da ita.

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *