News
Kotu ta yi watsi da roƙon da Muhuyi Magaji ya shigar na a hana ƴan sanda su kama shi
Daga yasir sani Abdullahi
A yau Talata ne Babbar Kotun Taraiya a Jihar Kano ta yi fatali da buƙatar da dakataccen Shugaban Hukumar Karɓar Ƙorafe-ƙorafe da Yaƙi da Cin-hanci da Rashawa ta Jihar Kano, Muhuyi Magaji Rimingado.
A roƙon da ya shigar gaban kotun, Riminga ya nemi kotun da ta hana kwamitin bincike da majalisar dokoki ta Kano ta kafa, da kuma hana ƴan sanda su bincike shi, tsare shi ko yi masa barazana.
Sannan ya roƙi kotun da ta bada umarnin kowa ya dakata ba tare da ɗaukar mataki kan takardun shaidar lafiya na biyu da a ke zargin yayi amfani da su.
Da ta ke yanke ƙwarya-ƙwaryan hukunci a yau Talata, Mai Shari’a Jane Inyang, ta ce kwamitin bincike da aka kafa da kuma jami’an tsaro suna da iko da doka ta basu na su binciki Rimingado.
Inyang ta kuma yanke cewa babu hurumi na jaddada ko yin watsi da hukuncin da kotu mai hurumi iri ɗaya ta yi da wacce a ka miƙa wa ƙorafi ta yi.
Ta kuma ce kamata ya yi Rimingado ya shigar da ƙorafi a kan yan majalisar dokoki a Babbar Kotun Jiha ba ta taraiya ba.
-
News4 days ago
Matasa A Unguwar Gama Sun Yi Kira Ga Majalisar Dokokin Kano Ta Ladabtar Da Ɗan Majalisar Nassarawa Kan Zargin Cin Zarafin Gwamna
-
News4 days ago
Shugaba Tinubu Ya Ce Ba Zai Dawo Da Tallafin Man Fetur Ba Kuma Ba Ya Da-na-sanin Cire Shi
-
News4 days ago
DSS Ta Gurfanar Da Mutum Biyar Gaban Kotu Bisa Zarginsu Da Garkuwa Da ‘Yan NYSC 20 A Imo

