News
Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi Allah wadai da mamayar Rasha a Ukraine

Daga Muhammad Muhammad Ibrahim
Ƙasashe mambobin Majalisar Ɗinkin Ɗuniya sun kada kuri’a da gagarumin rinjaye ta nuna kyama ga mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine, inda suka nemi janyewarta nan take.
Ayayin taron na gaggawa wanda ba kasafai ake irinsa ba, Rasha ta kare matakinta na mamayar makwabciyarta, tana musanta cewa ta aikata laifin yaki, tare da zargin ƙasashen yamma da matsa wa da kuma barazana ga kasashe kan su jefa kuri’ar amincewa da matakin , ba tare da ta bayar da wata sheda ba.
Ƙasashe 141 suka amince da kuɗirin daga cikin mambobin majalisar 193 a babban taron na Majalisar Ɗinkin Duniya
Ƙasashje 35 suka kaurace wa kuri’ar, ciki har da Rasha da Indiya.
Rahoton ya kuma yi Allah-wadarai kan yadda Shugaba Putin na Rasha ya sanya dakarun nukiliya na kasarsa cikin shiri.
Wannan ne taron gaggawa na farko tun 1997.
Ƙasashe biyar ne suka kaɗa ƙuri’ar ƙin amincewa da kudirin yin Allah wadai da Rasha.
Bai zo da mamaki ba da Belarus babbar aminiyar Rasha ta bayyana adawa da kuɗirin. Wasu dakarun Rasha ta Belarus suka kutsa Ukraine.
Syria ma babbar aminiyar Rasha ta ƙi amincewa da ƙudirin.
Haka ma Eritrea daga Afirka da Koriya Ta Arewa daga yankin Asiya da suka ƙi amincewa da ƙudirin.
China ta ƙauracewa zaman kaɗa ƙuri’ar[wpstatistics stat=pagevisits time=week provider=Gh format=Yhh id=Gg]