Connect with us

News

Shugaban NNPP na Kano ya yi barazanar zuwa kotu bayan da uwar jam’iya ta naɗa Doguwa a matsayin shugaban riƙo

Published

on

FB IMG 1646319011970
Spread the love

Daga yasir sani abdullahi

 

 

Advertisement

Shugaban Jam’iyar NNPP a Jihar Kano, Hisham Habib, ya yi barazanar ɗaukar matakin Shari’a bayan da uwar jam’iyar ta ƙasa ta ta sauke shugabannin jam’iyar na jiha.

Jaridar indaranka ta fahimci cewa NNPP ta samu haɓɓaka a arewa kwanaki kaɗan bayan da sanarwar ta fita cewa tsohon gwamnan Kano, Rabi’u Musa Kwankwaso na shirin barin PDP zuwa jam’iyar ta NNPP.

A jiya Laraba ne Habib ya yi maraba da zuwan Kwankwaso, sai dai ya ce babu tabbacin samun takara ga sababbin shigowa jam’iyar.

Advertisement

A wata sanarwa da ya fitar a yau Alhamis, Habib ya ce matakin na rushe shugabannin da uwar jam’iyar ta yi wani ƙarfa-ƙarfa ne ga dimokuraɗiyya.

Ya ce wannan matakin bai dace ba kuma ba a bi hanyar nuna domokraɗiyya na haƙiƙa ba.

Habib ya koka da cewa idan har ƴan siyasa za su riƙa shigo wa jam’iya su ture waɗanda su ke ciki, to lallai siyasa ta shiga halin tsaka mai wuya.

Advertisement

Sabo da haka, Habib ya ce ya fara tuntuɓa domin ɗaukar matakin Shari’a ko kuma ya fice ma da ga jami’yar.

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *