News
Gwamnatin Ukraine na garkuwa da ɗaliban Afrika don kare kanta – Putin

Daga Muhammad Muhammad Zahraddin
Shugaban Rasha Vladmir Putin, ya ce da gangan hukumomin Ukraine ke garkuwa da ɗaliban Afrika da na sauran ƙasashen duniya da ke karatu a can, domin kare kansu.
Ɗaliban kasashen duniya sun yi ta zargin cewa jami’an Ukraine na hana su tsallaka iyaka don gujewa yaƙi.
Yayin wani jawabi da ya gabatar da yammacin nan, Mista Putin ya ce sun samu rahotannin da ke nuna cewa jami’an Ukraine na kashe ƴan ƙasashen waje, su kuma ɗaura alhakin hakan a kan Rasha.
Ya bada misali da wani abu da ya faru, inda ya ce sojojin Ukraine sun kashe wasu