Connect with us

News

A yanzu haka Nijeriya na da man fetur da zai kai kwanaki 32 bai ƙare ba — Minista

Published

on

Spread the love

Daga Muhammad Muhammad zahraddin

 

 

Advertisement

 

A yau Laraba a Abuja, Ministan Albarkatun Man Fetur, Timipre Sylva, ya baiwa Majalisar Zartaswa bayanai a kan adadin lita biliyan 1.9 na man fetur da ƙasar nan ke da shi a ajiye.

Ya ce yawan man ya ishi ƙasar nan har nan da kwanaki 32.

Advertisement

Ministan ya samu rakiyar Shugaban Kamfanin Man fetur na Ƙasa, NNPC, Mele Kyari wajen taron na majalisar zartaswa na mako-mako, wanda Mataimakin Shugaban Ƙasa, Yemi Osinbajo ya jagoranta.

A nashi ɓangaren, kakakin Mataimakin Shugaban Ƙasa, Laolu Akande, da ya ke zanta wa da manema labarai bayan kammala taron, ya ce NNPC ya lodin mai ba dare ba rana domin magance matsalar layi a gidajen mai.

Ya ce layika sun fara raguwa sosai a gidajen mai a Abuja, Kaduna da wasu manyan birane, inda ya ƙara da cewa gidajen mai da dama sun fara sayar da mai na awa 24.

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *