Connect with us

News

Ba tilasta wa waɗanda a ke zargi da kisan Hanifa su amsa laifin su a kai ba — Kotu

Published

on

Spread the love

Daga Muhammad Muhammad zahraddin

 

 

Advertisement

 

Babbar Kotun Jiha mai lamba 5, ƙarƙashin Mai Shari’a Usman Na-abba, ta yanke hukunci cewa iƙirarin da waɗanda a kae zargi da kisan Hanifa Abubakar su ka yi cewa jami’an tsaro ne su ka azabtar da su shi ya sa su ka amsa laifin, ba gaskiya ba ne.

Da ya ke yanke ƙwarya-ƙwaryan hukunci a kan hakan a yau Laraba, alƙalin kotun, Mai Shari’a Usman Na-abba ya ce bayanan da shaidu su ka bayar sun nuna cewa Abdulmalik Tanko, babban wanda a ke zargi da kisan Hanifa, da Hashimu Isyaku, wanda a ke zargi da sa hannu a kisan, ba tilasta musu a ka yi ba.

Advertisement

A cewar Na-abba, shaidun, waɗanda su ne jami’an da su ka yi bincike a kan laifin, sun yi wa Tanko da Isyaku tambayoyi ne a cikin ofisoshi kuma da mutane a cikin ofishin.

Ya ƙara da cewa ba bu wata hujja da Tanko ya bayar ta cewa an azabtar da shi, inda ya ce ya gaza fadin sunan ɗan sandan da ya ce ya mishi azaba, ya kuma kasa faɗin sunan na’urar da ya ce an riƙa ɗana masa a jikin sa.

A bisa haka ne Na-abba ya ce dukkan su wadanda a ke zargin, har da Fatima Jibrin, wacce ita dama ba ta de an dake ta ba, amma dai ta ce an tsorata ta, basu da hujjar cewa tilasta musu a ka yi su amsa laifin su.

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *