News
Ƴan jam’iyar APC da PDP 300,000 na shirin komawa NNPP a Jigawa
Daga maryam bashir musa
A ƙalla fusatattun ƴan jam’iyar mai mulki ta APC, da ta adawa ta PDP dubu ɗari uku ne ke shirin sauya sheƙa zuwa jam’iyar NNPP a Jihar Jigawa.
Shugaban NNPP na jiha, Gambo Ibrahim Alawo, shi ne ya baiyana haka a taron manema labarai da ya kira a yau Alhamis a Dutse, babban birnin Jigawa, jim kaɗan bayan wata ganawa da shugabannin jam’iyar su ka yi.
Ya ce a ganawar, shugabannin sun tattauna batun shigowar ƴan jam’iyun APC da PDP cikin NNPP da ga Ƙananan Hukumomi 27 na Jihar Jigawa.
Alawo ya ce jam’iyar NNPP na maraba-lale da duk mai sha’awar dawo wa cikinta, inda ya tabbatar da cewa za a riƙe duk wani ɗan jam’iyar da muhimmanci da kuma kula da hakkin sa cikin gaskiya da adalci.
“Mu na sane da cewa wasu jam’iyyu sun fara razana da mu, to mu wannan ba zai dame mu ba. Mu dai mu na man mu na ta shiri har sai mun karɓe mulki a Jigawa da Nijeriya baki ɗaya,” in ji Alawo.
Daily Nigerian Hausa ta gano cewa tun sanarwar da ta fita cewa tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso na kan hanyarsa ta shiga NNPP, jam’iyar na neman zama babbar yar adawa ta uku, musamman a arewacin Nijeriya.