Sports
Kasuwar ‘yan kwallo: Makomar Salah, Haaland, Suarez, Kessie, Kane, Hazard
Daga Muhammad Muhammad zahraddin
Mohamed Salah, bai zaku ba ya bar Liverpool a bazaran nan, maimakon haka zai bari har ya yanke shawarar tafiya a shekara mai zuwa a lokacin ba wani kwantiragi a kansa. (Fabrizio Romano)
Shi dai kocin kungiyar ta Liverpool Jurgen Klopp ba zai yi wata magana da Salah din ba ko wakilinsa yayin da ake dambarwa a kan sabuwar yarjejeniyar zama da kungiyar za ta kulla da dan wasan na Masar. (Mirror)
Tauraron dan wasan Borussia Dortmund dan Norway Erling Braut Haaland, zai bukaci a sanya sharadin kudin na-gani-ina-so a duk wata yarjejeniya da zai kulla ta tafiya wata kungiya nan gaba a bazaran nan. (Sun)
Luis Suarez, na son ya buga wasa akalla na karin shekara daya a Turai, kafin ya tafi gasar MLS ta Amurka, kuma tsohon dan wasan na Liverpool na duba yiwuwar sake komawa Ingila inda zai je Aston Villa. (Mail)
Manchester United ta amince ta kulla yarjejeniya da matashin dan wasan tsakiya na Brighton Toby Collyer mai shekara 18. (Mirror)
Matashi Collyer zai zauna a United tsawon shekara uku da rabi. (Express)
Dan wasan tsakiya na AC Milan dan Ivory Coast Franck Kessie mai shekara 25 zai kasance na farko da Barcelona za ta dauka a bazaran nan, sai kuma dan bayan Chelsea dan Denmark Andreas Christensen, mai shekara 25, ya biyo baya, dukkansu a kyauta, saboda ba wani kwantiragi a kansu. (ESPN)
Uefa ta bayar da tabbacin cewa wasan Chelsea na Zakarun Turai na zagayen kungiyoyi 16 karo na biyu da Lille zai wakana yadda ka tsara. (RMC Sport – in French)
Tauraron dan wasan Tottenham na Ingila Harry Kane, mai shekara 29, ya ce, yana samun kwarin guiwar kara bajinta da kwarewa a karkashin jagorancin kocinsu Antonio Conte, yayin da Manchester United ke nuna sha’awarsa. (Sky Sports, via Mirror)
Arsenal na fuskantar hamayya daga Real Madrid da Barcelona a kan dan wasan tsakiya na Napoli Fabian Ruiz mai shekara 25 dan Sifaniya. (Corriere dello Sport, via Express)
Haka kuma Arsenal din za ta yi kokarin hada fam miliyan 20 domin sayen sabon dan gaba, daga cinikin da za ta yi na sayar da dan wasanta na tsakiya dan Faransa Matteo Guendouzi, mai shekara 22, ga Marseille, da kuma dan Uruguay Lucas Torreira, ga Fiorentina. (Mirror)
Bugu da kari Gunners din sun kuma yi tuntuba a kan Eden Hazard na Real Madrid mai shekara 31. (Foot Mercato – in French)
Barcelona za ta nemi sayen dan wasan tsakiya na Wolves dan Portugal Ruben Neves, mai shekara 25, domin maye gurbin dan Sifaniya Sergio Busquets, mai shekara 33. (Mundo Deportivo – in Spanish)
Haka-zalika Barcelona na fatan ganin Chelsea ta bar dan bayanta Cesar Azpilicueta, dan Sifaniya mai shekara 32, ya bar Stamford Bridge a kyauta a bazaran nan. (ESPN, via Express)
Tsohon dan bayan Manchester United Rio Ferdinand yana ganin kungiyar ta Old Trafford za ta yi kokarin sayen dan bayan Paris St-Germain Marquinhos, dan Brazil mai shekara 27, da kuma Ronald Araujo na Barcelona dan Uruguay mai shekara 23, domin karfafa bayanta. (MEN)
