Gwamnatin Ethiopia ta musanta ikirarin Hukumar Lafiya ta Duniyana hana masu kai agaji shiga yankin Tigray, inda ake fama da rikici sama da shekara guda.
Shugaban WHO Tedros Ghebreyesus ya yi kira ga gwamnati ta bude hanyar da za a samu kai kayan agaji yakin Tigyar.
Amma ministan watsa labarai na kasar Legesse Tulu ya ce WHO kamata ya yi ta zargi mutanen yankin Tigray game da hana shigar da kayan agajin maimakon gwamnati.
Yace yan tawaye ne suka rufe hanyar da gangan.
An samu damar kai wasu kayan agajin yankin da rikicin ya fi kamari a baya, amma WHO ta ce akwai bukatar kari.

