News
Bashin da ake bin Najeriya ya doshi N40tr bayan karbo aron N6tr a shekarar 2021.
Daga Khadija Ibrahim Muhammad
Ofishim kula da bashi a Najeriya DMO ya ce bashin da ke kan wuyan gwamnati sun karu sosai a 2021.
Darekta-Janar ta DMO, Patience Oniha ta ce kudin da ake bin Najeriya ya karu daga N32.92tr a 2020 zuwa N38.56tr a shekarar 2021.
Patience Oniha tayi wannan bayani a lokacin da ta zanta da manema labarai a Abuja. Oniha ta ce wannan ya kunshi bashin gwamnatin tarayya da na jihohi.
An yi amfani da wannan bashi da aka karbo wajen cike gibin da aka samu a kasafin kudi tare da yin ayyukan more rayuwa da kuma farfado da tattalin arziki.
Duk da yawan bashin da ake ganin gwamnatin kasar nan ta na ci, shugabar ta DMO ta ce har yanzu idan aka kamanta yawan bashin da GDP, 22% ne rak.
Bankin Duniya ya kayyade cewa ka da nauyin bashin kasa ya zarce 55% na jimillar tattalin arzikinta. Kungiyar ECOWAS kuwa ta tsaida shi ne a kan 70%.
A shekarar bara, an ci bashin ne daga tsarin Eurobonds da Sukuk da sauransu. An kuma yi amfani da kudin domin ayi wa jama’a ayyuka.
Darekta-Janar ta DMO ta ce an kawo dokar Finance Act 2019 ne da nufin a kara yawan abin da ake samu ta haraji domin ganin an rage dogara da karbo bashi.
Oniha tace “Gwamnatin tarayya ta na lura da nauyin bashi ga kudin shigan gwamnati, kuma ta fara daukar matakan kara samun haraji da aka shigo da dokar kudi tun 2019.”
Bayanan da aka fitar ya nuna an kashe N612bn wajen biyan bashin gida tsakanin Junairu zuwa Maris a 2021. An kuma biya $1bn na bashin da aka karbo a waje.
Tsakanin Afrilu zuwa Yunin 2021, an kashe fiye da N447bn domin a biya bashi a gida da waje. Sannan an kashe N1.03tr da N429bn tsakanin Yuli zuwa Disamba.
