Entertainment
Allah zai sakawa yaran da kuka tura Almajiranci -Nafisa Abdullahi.
Daga Maryam Bashir Musa
Jarumar masana’antar Kannywood Nafisa Abdullahi ta caccaki masu haihuwa barkatai bisa yadda suke kasa daukar nauyin yaran da suka haifa.
A wani rubutu da jarumar ta wallafa a Twitter, tace mutane suna haihuwa yara barkatai domin kawai su turasu Almajiranci, don haka Allah zai sakawa yaran da aka haifa.
Nafisa Abdullahi ta nuna damuwa kan yadda yadda ake aikewa da yara yan shekara 2 zuwa 3 Almajiranci.
Yankin Arewacin Najeriya dai yayi shuhura wurin aikewa da yara Almajiranci, abinda ake ganin wasu na fakewa dashi domin haifar yaran da bazasu iya kulawa dasu ba.
Advertisements
