News
ISWAP ta yi iƙirarin kashe dakarun Najeriya uku a Jihar Borno
Daga kabiru basiru fulatan
ISWAP ta yi iƙirarin kashe dakarun Najeriya uku a Jihar Borno
Ƙungiyar Islamic State West Africa Province (ISWAP) mai iƙirarin jihadi ta yi iƙirarin cewa ta kashe mayaƙan sa-kai uku da ke aiki da rundunar sojan Najeriya a Jihar Borno da ke arewa maso gabashin ƙasar.
Kazalika, ta ce ta yi garkuwa da wasu ma’aikatan agaji na ƙungiyar Red Cross yayin harin da ta ce ta kai ranar Juma’a.
Ƙungiyar ta bayyana hakan ne ciikin wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na dandalin Telegram, tana mai cewa ta kai harin ne a garin Monguno.
Sai dai ƙungiyar kan kira wasu mutane da ta kama da cewa ma’aikatan Red Cross ne ko da kuwa ba natan ba ne.
- A watan Agustan 2020 ne ƙungiyar ta ayyana yaƙi a kan ma’aikatan agaji da ke aiki a Jihar ta Borno, tana mai zargin su da aiwatar da ayyukan abinda suka kira “rusa Musulunci”.
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
