News
Buhari Ya Nada Sabbin Ministoci
Daga kabiru basiru fulatan
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya nada sabbin minsitoci, sa’o’i kadan bayan ’yan bindiga sun kai wa ayarin motocinsa hari a mahaifarsa Daura.
Nadin na zuwa ne sa’o’i bayan wani hari da aka kai wa Gidan Yarin Kuje da ke Abuja, inda maharan suka kashe mutum biyu a cikin ayarin.
Buhari ya sanar da sauye-sauyen ne a zaman Majalisar Zartarwa ta Tarayya a Fadar Shugaban Kasa ranar Laraba.
A lokacin zaman ne ya rantsar da sabbin ministocin bayan Majalisar Dattawa ta tantance su a makon jiya.
Yanzu-Yanzu: Abba Kyari, Dariye, Nyame sun tsere daga magarkamar Kuje a wani hari
Rukunin farko na sabbin ministocin da ya rantsar su ne: Henry Ikechukwu Ikoh (Abia) da Umana Okon Umana (Akwa Ibom) da Odum Odih (Ribas) da kuma Ademola Adewole Adegoroye (Ondo).
Na biyun kuma su ne: Umar Ibrahim El-Yakub (Kano) da Goodluck Nnana Opiah (Imo) da kuma Egwumakama Joseph Nkama (Ebonyi).
Kafin rantsarwar taron ya yi shiru na minti daya domin nuna jimamin rasuwar Sakatare-Janar na Kungiyar Kasashe Masu Arzikin Mai (OPEC) mai barin gado, Muhammad Barkindo, wanda ya rasu a cikin dare.
Rasuwar Barkindo ta auku ne a ranar da ya yi wata ganawa da Shugaba Buhari, wanda ya yabe shi a matsayin wakili abin alfahari ga Najeriya.
Barkindo ya rasu yana da shekara 63 a duniya kuma shi ne Sakatare-Janar na OPEC na hudu, daga Najeriya.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
