Connect with us

News

Shirin Inganta Rayuwa: Gwamnatin Tarayya Za Ta Rabawa Matan Karkara Naira Dubu 20.

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

Gwamnatin tarayya ta ce ta kammala shirye-shiryen fara bayar da Naira 20,000 ga duk matan karkara a fadin kasar nan a kokarin shirin gwamnati na Inganta rayuwar ‘yan kasa (NSIP).

 

Advertisement

 

Mataimakin Kakakin Majalisa ya goyi bayan gaggauta haramta baburan acaɓa a ƙasar nan.

Advertisement

An bullo da shirin bayar da tallafin ne ga ‘yan kasa masu raunin tattalin Arziki a shekarar 2020 don Inganta rayuwarsu da gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ke yi a karkashin shirin fitar da ‘yan Nijeriya miliyan 100 daga kangin talauci.

Ministar kula da jin kai da bala’o’i da ci gaban jama’a Sadiya Umar Farouq ce ta bayyana hakan a ranar Laraba a Abuja yayin wani taron manema labarai da masu ruwa da tsaki kan aiwatar da tallafin ga mabukata.

Advertisement

Farouq ta ce an yi wannan tallafin ne domin bayar da tallafi ga mata masu fama da talauci a yankunan karkara dake kasar nan.

“Za a raba tallafin kudi na N20,000.00 ga mata da maza masu fama da talauci a fadin Jihohi 36 na tarayya da babban birnin tarayya,” inji ta.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending