Connect with us

News

Mun Ba Buhari Wa’adi Kan Batun Tsaro – Bangaren Adawa.

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAH 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

A ci gaba da cece kucen da ake yi game da tabarbarewar yanayin tsaro a Najeriya, ‘yan adawa sun ce sun bai wa Buhari wa’adin kawo karshen aika aikar ‘yan ta’adda ko kuma su tsige shi.

 

Advertisement

Shugaban marasa rinjaye na majalisar dattawa, Sanata Phillip Aduda, ya bayyana matsayin ‘yan majalisar ne a ranar Laraba yayin da yake ganawa da manema labarai a zauren majalisar a babban birnin tarayya, Abuja.

Shirin Inganta Rayuwa: Gwamnatin Tarayya Za Ta Rabawa Matan Karkara Naira Dubu 20.

Advertisement

Kafin gabatar da jawabai, ‘yan majalisar daga jam’iyyun adawar sun fice daga zauren majalisar dake zama bayan yin kiran a tsige shugaban kasa Muhammadu Buhari a zauren majalisar na jiya Laraba.

 

Advertisement

Sanata Aduda ya gabatar da wani batu inda ya nemi shugaban majalisar dattawa, sanata Ahmad Lawan, da ya yi tsokaci a kan batun tsaro a kasar nan da kuma batun tsige shugaba Buhari.

 

Advertisement

Sai dai Sanata Lawan, wanda ya jagoranci zaman majalisar ya ki amincewa da bukatar shugaban marasa rinjayen jam’iyyar PDP din, yana mai cewa batun tsarin da aka taso bai da tushe balle makama.

 

Advertisement

Daga bisani bayan fusata da matakin da shugaban majalisar dattawan ya dauka, duk ‘yan majalisar da aka zaba a karkashin inuwar jam’iyyun siyasa ban da jam’iyyar APC mai mulki sun bi sahu su ficewa daga zauren majalisar yayin da zaman majalisar ke ci gaba da gudana.

 

Advertisement

Batun ficewar dai na zuwa ne a cikin jerin shiga damuwa da ‘yan Najeriya da kungiyoyi daban-daban suka nuna a yayin da matsalar rashin tsaro ke kara ta’azarra a kasar.

 

Advertisement

Daga farko dai, wani mai rajin kare hakkin bil’adama, Farfesa Chidi Odinkalu, ya soki gwamnatin da shugaba Muhammadu Buhari ke jagoranta kan yadda take tunkarar kalubalen tsaro a kasar.

 

Advertisement

Sai gamayyar kungiyoyin arewacin Najeriya, Kungiyar kwadago ta Najeriya da saura kungiyoyi masu fafutukar kare hakkin bil’adama dake ta yin kiraye-kirayen shugaban ya sauya salon yaki da matsalolin tsaron da suka addabi kasar da ma sauran matsaloli kamar a fannin ilimi, yaki da talauci da kuma farfado da komada tattalin arziki da dai sauransu.

 

Advertisement

A wani bangare kuma, a jiya ne kwana na biyu a zanga-zangar kungiyar kwadago ta Najeriya inda kungiyar ta yi tattaki zuwa majalisar dattawa don nuna rashin jin dadin al’umma agame da yadda gwamnati ke yiwa fannin ilimin kasar rikon sakainar kashi.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending