Sports
Banzema ya lashe kyautar gwarzon ɗan wasan UEFA na shekara
Daga: Muhammad Muhammad zahraddin
Kungiyar Kwallon Kafa ta Nahiyar Turai ta bayyana kyaftin ɗin Real Madrid, Karim Benzema a matsayin gwarzon dan wasan UEFA na bana.
Bafaranshen ya lashe kyautar ne a saman abokin wasansa, Thibaut Courtois da Kevin De Bruyne na Manchester City.
Benzema ne ke kan gaba wajen cin kwallaye a kakar wasan da ta gabata a gasar zakarun Turai da ƙwallaye 15.
Ɗan wasan mai shekaru 34 shi ne wanda ake sa ran zai lashe kyautar Ballon d’Or, kyauta Mafi daraja a duniyar ƙwallon ƙafa a karshen wannan shekara.
Benzema ya taka rawar gani yayin da Madrid ta lashe kofin La Liga ta bana, inda ta kare da maki 13 a saman abokiyar burmin ta, Barcelona.
Ya zura kwallaye 35 a wasanni 37 yayin da kungiyar ta kashe gasar La Liga ta bana a ƙarƙashin jagorancin Carlo Ancelotti.
