Sports
Abin da ya kamata ku sani ranar rufe kasuwar cinikin ‘yan wasa a Premier
DAGA: MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Daren ranar Alhamis za a rufe kasuwar saye da sayar da ‘yan kwallon kafa a wasu kasashe a nahiyar Turai har da Ingila – Mohammed Abdu ya hada muku abubuwan da ya kamata ku sani kan cinikayyar da aka yi.
Kasuwar bana ta Premier League ta fara ci ranar 10 ga watan Yunin 2022, da zarar an kammala cinikayyqar ranar Alhamis 1 ga watan Satumbar 2022 – sai ranar 1 ga watan Janairun 2023 za a sake bude kasuwa.
Tuni kungiyoyin Premier League sun kashe kudi kusan £1.7bn a kasuwar saye da sayar da ‘yan kwallo da za a kammala hada-hada a tsakar daren Alhamis.
A kakar 2017 aka yi cefane mai tsada kan £1.43bn.
An samu karin cinikayya bayan cutar korona da ta kai tsaiko a kaka biyu baya musamman karancin rashin samun kudin shiga ga kungiyoyin – an kashe £1.1bn a bara.
Kungiyoyi bakwai a Premier sun dauki ‘yan wasa a matakin mafi tsada a tarihin kafuwarsu kan kudi sama da £30m kowanne a kakar cinikayya ta 2021.
Za a rufe kasuwar saye da sayar da ‘yan kwallo a English Premier League da kuma Football League teams da karfe 23:00 GMT ranar Alhamis 1 ga watan Satumba, awa daya tsakani a rufe ta Scotland.
A kasar Sifaniya, inda Barcelona ta kashe dan karen kudi wajen sayen ‘yan kwallo a bana, za a rufe kasuwar da karfe 23:00 a Faransa kuwa da karfe 22:00.
Za a rufe kasuwar Italiya da karfe 19:00 ta Jamus kuwa za ta watse da karfe 17:00 ranar Alhamis.
Cefanen da aka yi a gasar Premier League:

Manyan kungiyoyin Premier League sun dauki ‘yan kwallo 143 – fiye da 128 da aka saya a 2019 da 132 da aka dauka a 2020.
A bara an sayi ‘yan wasa 14 a ranar karshe da za a rufe kasuwa – mafi karanci da aka yi hada-hada a ranar karshe ta rufe kasuwar saye da sayar da ‘yan kwallo.
Tuni Manchester United ta kulla yarjejeniyar da Ajax, domin daukar dan kwallon Brazil, Antony, mai shekara 22.
Idan United ta kammala cinikin da ake cewar zai kai £81.3m – zai zama na hudu da aka saya da tsada a tarihin gasar Premier League.
Kociyan United, Erik ten Hag, wanda ke daf da daukar mai tsaron ragar Newcastle United, Martin Dubravka, na sa ran Cristiano Ronaldo zai hakura ya karasa kwantiraginsa, bayan da yake son buga Champions League a kakar nan.
Idan cinikin Antony ya kammalu – Manchester United za ta kashe sama da £210m domin ganin Erik ten Hag ya taka rawar gani – ta dauki dan wasan Feyenoord mai tsaron baya, Tyrell Malacia da mai tsaron bayan Ajax, Lisandro Martinez da mai buga wasan tsakiya daga Real Madrid, Casemiro – da wanda kwantiraginsa ya kare a Brentford a kakar da ta wuce Christian Eriksen.
Wani cinikin da ake ganin da kyar idan za a yi shi ne na Anthony Gordon, wanda Chelsea ke son dauka daga Everton.

Tun farko Everton ta yi watsi da tayin £40m da kungiyar Stamford Bridge ta yi wa dan kwallon.
Ita kuwa Manchester City na kokarin sayen dan wasan Borussia Dortmund, mai tsaron baya, Manuel Akanji, wanda ake cewar kudinsa zai kai £15m.
Ko Liverpool za ta kara cefane kuwa? tuni Jurgen Klopp ya ce ya kamata su kara shiga kasuwa, bayan da masu buga masa tsakiya da dama ke jinya.
Ko Leicester za ta dauki fitatcen dan wasa kuwa? Alex Smithies ne kadai ya koma King Power a matakin mai tsaron raga na uku a kungiyar.
Chelsea ta kashe kudi mai yawa a tarihin kungiyar kan £248m a bana, bayan sayen mai tsaron bayan Leicester City, Wesley Fofana kan £70m ranar 31 ga watan Agusta.

Transfermarkt wadda ke kan intanet da ake ganin kimarta ta ce Manchester City da West Ham da Tottenham da Nottingham Forest da Newcastle da Arsenal da Manchester City da kuma Wolves sun kashe sama da £100m kowacce a kakar nan – tara kenan daga 12 da ke kan gaba a kashe kudin sayen ‘yan kwallo a nahiyar Turai.
Kungiyoyi bakwai ne suka kafa tarihin sayen dan wasa mafi tsada a tarihinsu a bana.
Liverpool ta dauki dan kwallon Benfica, Darwin Nunez kan £64m zai kuma kai £85m, ita kuwa Newcastle ta dauki dan wasan Real Sociedad mai cin kwallaye, Alexander Isak kan £60m.
Tottenham ta sayi dan kwallon Brazil, Richarlison daga Everton kan £60m.

Wolves ta dauki dan kwallon Sporting Lisbon mai taka leeda daga tsakiya, Matheus Nunes a matakin mafi tsada da ta saya kan £38m.
Brentford da Nottingham Forest ba a barsu a baya ba, wajen sayen ‘yan wasa da tsada a tarihi a kakar nan.
Brentford ta sayi dan kwallon Bologna mai tsaron baya, Aaron Hickey kan £17m da dan kwallon Hull, Keane Lewis-Potter kan £20m.
Ita kuwa Forest ta sayi dan wasan Union Berlin, Taiwo Awoniyi kan £17m da dan wasan Watford, Emmanuel Dennis kan £20m – sannan ta sayi dan wasan Wolves, Morgan Gibbs-White kan tsakanin £25m zuwa £42m – ta dauki ‘yan wasa 18 a kakar nan.
West Ham ta sayi dan wasan tawagar Brazil mai taka leda a Lyon, Lucas Paqueta kan £36.5m – amma zai iya kaiwa £50m idan aka hada da kudin tsarabe-tsarabe.

Leeds United ta dauki dan kwallon Red Bull Salzburg, Brenden Aaronson kan kudin da ake cewar zai kai £26m kamar yadda ta sayi Rodrigo mafi tsada a tarihi.
Akwai ciniki da aka yi mai tsoka a kakar nan da suka hada da daukar dan kwallon Brighton, Marc Cucurella da Chelsea ta saya £60m da dan kwallon Manchester City, Raheem Sterling kan £50m – yanzu kuma ta sayi Fofana.
Manchester City ta sayi Erling Haaland daga Borussia Dortmund kan £51.2m da dan wasan Leeds, Kalvin Phillips kan £45m.
Arsenal ta dauki dan kwallon tawagar Brazil, Gabriel Jesus daga Manchester City kan £45m.

Bayan wannan cefanen da aka yi a bana – wa zai lashe kofin Premier League na bana?
An buga wasannin mako na biyar kawo yanzu, in banda wanda Leicester City za ta karbi bakuncin Manchester United ranar Alhamis.
Manchester City ce ta lashe Premier League a 2021/22 da tazarar maki daya tsakaninta da Liverpool a ranar karshe da aka rufe wasannin.
Kawo yanzu Arsenal ta ci wasa biyar a jere tana ta daya da maki 15, ita ce kadai ta yi wannan bajintar a kakar nan.
Erling Haling ya ci wa Manchester City kwallo tara a wasa biyar da fara kakar nan, har da uku rigis sau biyu a jere.
Ko fitila ta haska wadda za ta lashe kofin bana kuwa da wanda zai lashe takalmin zinare a matakin wanda zai fi kowa cin kwallaye a kakar nan?
