Connect with us

Sports

Liverpool ta sha da kyar a hannun Newcastle a Anfield

Published

on

Liverpool

DAG: MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN

Liverpool ta yi nasara a kan Newcastle da ci 2-1 a wasan mako na biyar a gasar Premier League da suka ranar Laraba a Anfield.

Advertisement

Alexander Isak ne ya fara ci wa Newcastle kwallo a minti na 38 da fara wasan, hakan suka je hutu Newcastle da kwallo daya.

Bayan da suka huta suka koma zagaye na biyu ne Liverpool ta farke ta hannun Roberto Firmino, sanann daf da za a tashi daga karawar Fabio Carvalho ya ci wa Liverpool na biyu.

Advertisement

Liverpool ta yi wasa 26 a gida a jere a Premier League kenan ba tare da an doke ta ba, wadda ta ci 20 da canjaras shida a Anfield tun bayan 1-0 da Fulham ta yi mata ranar 7 ga watan Maris din 2021.

Liverpool ta yi nasara a wasa 11 daga 12 da ta buga a baya a tsakiyar mako da yin nasara a karawa bakwai baya da cin kwallo 20 aka zura mata uku.

Advertisement

A kakar bara a Premier League Newcastle ta yi rashin nasara a wasa shida da kungiyoyin shidan farko a teburi da cin kwallo shida aka zura mata 20 a raga.

Eddie Howe ya yi rashin nasara a wasa na tara a jere a hannun Liverpool tun bayan 2-2 da suka tashi a Anfield a Afirilun 2017 a lokacin yana Bournemouth.

Advertisement

Liverpool ta ci Newcastle United kwallo 111 a gasar Premier, kungiyar da ta zazzagawa kwallaye mafi yawa a wasannin kenan.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending