Connect with us

News

WAEC ta ƙaryata rahoton cewa ta na ɗaukar ma’aikata

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

Hukumar shirya Jarrabawar Kammala Makarantun Sakandire ta Afirka-ta-Yamma, WAEC, ta nesanta kanta daga rahotannin da wasu kafafen yaɗa labarai suka fitar na cewa ta na neman ma’aikata.

 

Advertisement

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mukaddashiyar Shugabar sashen Hulɗa da Jama’a, Moyosola Adesina, da aka rabawa manema labarai a yau Juma’a a Legas.

Za muyi Nazarin hukuncin Kotun Daukaka Kara, mu Sanar da mataki na gaba – ASUU

Advertisement

Adesina ta gargadi jama’a da su yi hattara da ayyukan ƴan damfara, ta na mai cewa rahoton ba da ga gare ta ba ne.

 

Advertisement

A cewarta, rahoton ƙarya ne kuma yaudara ce.

 

Advertisement

“An jawo hankalinmu ga wani labari da a ke yaɗa wa cewa WAEC na daukar ma’aikata na ɓangaren karatu da ɓangaren ayyukan yau da kullum ta yanar gizo a dukkan kasashe biyar da ke ƙarƙashin mu.

 

Advertisement

“A nan WAEC na son sanar da masu ruwa da tsaki da sauran jama’a cewa wannan rahoton na bogi ne kuma ba da ga gare mu ya fito ba.

 

Advertisement

“Saboda haka, ana shawartar jama’a da su yi watsi da rahoton, domin karya ce, da nufin zaluntar al’umma.

 

Advertisement

“Don Allah, kuma lura cewa majalisar ta na buga tallace-tallacen ɗaukar ma’aikata ne kawai ta hanyar jaridu na kasa, gidan yanar gizon hukuma: https://www.waecnigeria.org/ da duk dandamalin kafofin watsa labarun,” in ji Adesina

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending