News
ASUU ta dakatar da yajin aikin bayan watanni takwas
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Kungiyar Ma’aikatan Jami’o’i ta dakatar da yajin aikin da ta kwashe watanni takwas ana yi, kamar yadda PUNCH ta tabbatar.
Duk da cewa kungiyar ba ta fitar da sanarwar a hukumance ba, wakilinmu ya tattaro cewa an dauki matakin ne a karshen taron majalisar zartarwa ta kasa da aka gudanar a sakatariyar ASUU da ke Abuja.
Ma’aikatan Jinya Sun Bai Wa Gwamnati Mako Daya Ta Biya Su Hakkokinsu
Da yake zantawa da wakilinmu, wata majiya mai cikakken bayani a cikin hukumar ta NEC ta ce, “Eh, an dakatar da shi”.
Da aka nemi karin bayani, majiyar ta ce, “Shugaban zai fitar da wata sanarwa a hukumance da safe”.
Jaridar PUNCH ta ruwaito cewa kungiyar malaman ta fara yajin aikin ne a ranar Litinin 14 ga watan Fabrairu, 2022.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
