News
Farashin tikitin jirgin sama ya ninka a Najeriya cikin shekara daya
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Hukumar kididdiga ta Najeriya – NBS ta ce farashin tikitin jirgin sama ya tashi da kashi fiye da 96 cikin 100 a cikin shekara daya.
A cikin rahotonta na watan Satumba, hukumar ta ce fasinjan jirgin sama na biyan kusan naira dubu 37 a cikin watan Satumbar 2021 amma kuma a watan Agustan bana ana biyan akalla naira dubu 65 wanda ke nuna tashin farashin tikitin.
Kyawawan Manufofi Da Dabarun Siyasar Da Na Koya Daga Kwankwaso – Sha’aban
Rahoton ya ce an samu dan karin kadan a farashin hawa motoci haya da kashi biyu cikin 100 daga shekarar da ta wuce zuwa bana.
Rahoton na hukumar NBS ta ce a bangaren sufurin babur ko kuma acaba babu wani bambamci sosai tsakanin bara da bana saboda karin bai wuce kashi daya cikin 100 ba.
-
News5 days ago
Jami’an Ƴansanda Sun Cafke Mai Safarar Makamai, Sun Kwato Harsasai 637 A Kaduna
-
News7 days ago
Jami’an NSCDC Sun Cafke Mutane Biyu Da Saniyar Da Ake Zargin Ta Sata Ce A Kano
-
News4 days ago
2027: INEC Ta Tabbatar Da Ibrahim Ali Amin Little A Matsayin Ɗan Takarar Gwamnan Kano A Jam’iyyar ADC
