News
Kyawawan Manufofi Da Dabarun Siyasar Da Na Koya Daga Kwankwaso – Sha’aban
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Ɗan takarar gwamnan jihar Kano a jam’iyyar ADP Malam Sha’aban Ibrahim Sharaɗa ya ce ya koyi ƙulumboto da dabarun siyasa masu yawa daga tsohon gwamnan Kano Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso.
Kwankwaso Ya Bude Makaranta A Garin Da Suka Shafe Shekara 30 Babu Makaranta
Malam Sha’aban ya bayyana hakan ne a wani saƙon taya murnar cika shekaru 66 ga tsohon ministan tsoron Najeriya Rabi’u Kwankwaso yayi a ranar 21 ga watan Oktoban 2023. A jawabin da aka rabawa manema labarai a Kano.

Sha’aban Ibrahim Sharaɗa wanda yanzu shi ne ɗan majalisar wakilai mai wakilta birnin Kano a majalisar tarayya, ya ce “tabbas irin nasarorin da Kwankwaso ya samu lokacin da yake gwamnan Kano daga 1999 zuwa 2003 da 2011 zuwa 2015 abu ne na musamman kuma mai muhimmanci da za a yi koyi da shi musamman ta fuskar gina ɗan Adam da samar mayan ayyukan more rayuwa.”
Haka zalika, fannin samar da tallafin zuwa karatu ƙasashen ƙetare na daga cikin dabaru da salon da nake koyi da su daga tsofaffin gwamnonin da suka shuɗe, kamar ayyukan gwamna Malam Ibrahim Shekarau na gina ɗan Adam da wasu ayyukan cigaban.
Sha’aban ya ƙara da cewa “tun daga lokacin da ya zamo ɗan majalisa a 2016 na himmatu wajen bayar tallafi ga mutane kusan dubu ɗari (100,000) waɗanda suka haɗar da matasa da mata a fannin sana’o’in da hanyoyin dogaro da kai.”

“Kusan ɗalibai 100 ne masu ƙaramin ƙarfi suka samu tallafin karatu zuwa ƙasar Sudan domin karantar fannoni daban-daban ƙarƙashin gidauniyar Sha’aban Ibrahim Sharada foundation.” A cewar Sha’aban.
Ɗan takarar gwamnan ya bayyana cewa “duk aiyukan ɗaukar nauyin karatu da koya sana’o’in yayi su ne da ɗan abinda yake da shi ba tare da tallafi ba.”Don haka ne yayi alƙawarin zai kawo sauyi babba a fannin ilimi ta hanyar cigaba da bayar da tallafin zuwa karatu ƙasashen waje idan yayi nasara a zaɓen gwamna 2023.
Haka kuma zai tabbatar da an inganta manyan makarantun da jihar Kano take da su a cikin gida ta hanyar samar kayan aiki da gine gine.
Daga ƙarshe sanarwar da Abbas Yushau Yusuf wanda shi ne mai magana da yawan ɗan takarar a jam’iyyar ADP ya rattabawa hannu ta bayyana murna a madadin Malam Sha’aban, ɗimbin magoya bayan jam’iyyar ADP, iyalansa, da mutanen mazaɓar yankin birni ga dan takarar shugabancin kasar nan Rabi’u Musa Kwankwaso bisa cika shekaru 66 da haihuwa.
Kana kuma ya jinjinawa Kwankwason akan samar da Sadaƙatul jariya ga mahaifinsa.
Sannan yayi addu’ar Allah yayi masa jagora ya kuma gafartawa mahaifinsa marigayi Majidadin Kano.
LABARAI 24
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
