Connect with us

News

Hukumar ICPC Ta Gurfanar Da Tsohon Shugaban Hukumar NABDA A Gaban Kotu Kan Zambar Naira Miliyan 400

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

Hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa da sauran laifuffuka masu alaka ICPC, ta gurfanar da tsohon shugaban riko na hukumar bunkasa fasahar kere-kere ta kasa NABDA, Farfesa Alex Akpa, a gaban kuliya bisa tuhume-tuhume 4 da suka hada da zamba, cin zarafi da aiki da mukami sauran laifuffuka masu alaka.

Advertisement

An dakatar da Farfesa Akpa ne tare da Famous Daunemigha da Wesley Ebi Siasia, tsohon mamba, kwamitin gudanarwa kuma tsohon darektan kudi da asusu na hukumar.

Ƴan Nijeriya ba su da hujjar da za su yi kukan yunwa, in ji Buhari

Advertisement

ICPC a karar da ta shigar gaban Honourable Justice Inyang Ekwo na babbar kotun tarayya da ke Abuja, ta zargi wadanda ake tuhuma da karkatar da kudaden da suka kai Naira miliyan 400 da aka ware domin kafa cibiyoyin raya albarkatun kasa a jihohi hudu na tarayya.

An kuma sanar da Kotun yadda aka raba kudaden da tsohon mukaddashin DG din ya yi ikirarin cewa shi ne asusu na shiga tsakani na hukumar kula da fasahar kere-kere, a tsakanin mutane ukun da suka kai Naira miliyan 260, Naira miliyan 50 da kuma Naira miliyan 40.

Advertisement

Lauyan ICPC, Golden Iwuagwu, ya kuma shaida wa Kotun cewa Hukumar ta shirya shaidu bakwai da za su ba da shaida kan wadanda ake tuhuma.

Laifin da ake zarginsu da aikatawa ya sabawa sashe na 18 (2) (d) kuma ana iya hukunta su a karkashin sashe na 18 (3) na dokar hana safarar kudade da haramtacciyar kasa, 2022.

Advertisement

Wadanda ake tuhumar duk sun “Musunta aika Laifin” lokacin da aka karanta musu kushin tuhume-tuhumen.

Sakamakon haka ne alkalin kotun ya bayar da belinsu bisa sharuddan belin gudanarwa da ICPC ta bayar a baya.

Advertisement

Alkalin kotun ya kuma umurci masu gabatar da kara da su mika wa magatakardar kotun cikin kwanaki bakwai takardun belin da ICPC ta yi wa wadanda ake kara.

An dage ci gaba da sauraren karar zuwa ranakun 6, 7 da 8 ga watan Maris, 2023.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending