Connect with us

News

Ana ci gaba da neman goyon bayan masu kada kuri’a a zaben rabin wa’adi a Amurka

Published

on

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN 

 

Advertisement

 

Jiga-jigan jam’iyyar Republican da takwarorinsu na Democrat a Amurka na kara azama domin ganin sun samu goyon baya yayin da ya rage kasa da sa’o’i 48 a kada kuri’a a zaben rabin wa’adi na ‘yan majalisun dokokin kasar.

Advertisement

 

Zaben na da muhimmanci ga Shugaba Joe Biden da kuma wanda ya gada Donald Trump.

Advertisement

Somaliya ta haramta amfani da kalmar ‘al-Shabab’ kan kungiyar ‘yan ta’adda

BBC ta rawaito cewa Kuri’ar jin raayi ta nuna cewa Republican za ta sake samun rinjaye a majalisar wakilai .

Advertisement

 

Yayin da hasashe kuma ya nuna cewa sakamakon wasu jihohin da ba a da tabbas game da wanda zai yi rinjaye a cikinsu, shi ne zai tabbatar da jamiyyra da za ta samu rinjaye a majalisar dattawa.

Advertisement

 

Masu kada kuri’a sun bayar da fifiko kan batun tattalin arziki, ‘yan Democrat na mayar da hankali kan batun zubar da ciki da mallakar bindiga, yayin da ‘yan Republican ke mayar da hankali kan karuwar miyagun laifuka, da kwararar baki da hauhawar farashi

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending