Sports
Ronaldo zai jagoranci tawagar Portugal a gasar Kofin Duniya
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Cristiano Ronaldo zai fafata a gasar cin kofin duniya a karo na 5 kenan a rayuwarsa ta kwallon kafa, bayan da Portugal ta sanya shi a cikin tawagar da za ta wakilci kasar a gasar da za a yi a Qatar.
Da ma an sa ran a sanya dan wasan mai shekaru 37, wanda shi ne dan kwallon da ya fi cin kwallaye a wasan tamola a wasannin kasa da kasa da kwallaye 117 a cikin tawagar da za ta wakilci Portugal, sai dai ba ya cikin ganiyarsa a daidai wannan lokaci.
Kwallaye 3 ne kawai Ronaldo ya ci daga wasanni 16 da ya buga a dukkan gasa, kuma wasannin gasar Firimiyar Ingila 4 ne kawai aka fara da shi a wannan kaka.
Tun da farko tsohon dan wasan na Real Madrid da Juventus ya mika bukatar barin United a farkon wannan kaka, amma abin ya fasakara, duba da cewa babu wata kungiya da ta nuna sha’awar aiki da shi.
Sai da ma kocin United Erik Ten Hag ya ajiye shi a benchi bayan da ya ki yin wasa a lokacin da aka sanya shi daga baya a
-
News7 days ago
Ƙungiyar ’Yan Kasuwar Wayoyi Ta Buƙaci NCC Ta Dakatar Da Tsarin Tantance Wayoyi Na DMS Tsawon Kwanaki 90
-
News4 days ago
Matasa A Unguwar Gama Sun Yi Kira Ga Majalisar Dokokin Kano Ta Ladabtar Da Ɗan Majalisar Nassarawa Kan Zargin Cin Zarafin Gwamna
-
News4 days ago
Shugaba Tinubu Ya Ce Ba Zai Dawo Da Tallafin Man Fetur Ba Kuma Ba Ya Da-na-sanin Cire Shi

