News
Kotu : tuhumar mutane 26 bisa laifin satar danyen Mai
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Wata kotu a nigeria tana tuhumar mutane 26 bisa laifin hada Baki wajen satar danyen Mai ba bisa ka,idaba bayan,da hukumone suke zargin jirgin Dakon Mai
Bisa bukatar hukumar nigeria ta kasar Equatorial Guinea ta tsare jirgin mai suna Heroic Idun, mai dauke da ganga miliyan 2 na mai a ranar 17 ga watan Agusta, bisa laifin tafiya ba tare da wata tuta ba, ya kuma tsere daga hannun sojojin ruwan Najeriya, ya yi tafiya a cikin ruwan Equatorial Guinea ba tare da izini ba.
Kwamitin wanzar da zaman lafiya ya ja kunnen ƴan takarar shugaban Najeriya
Mutanen 26 da suka hada da kyaftin din, sun gurfana a wata babbar kotu da ke birnin Fatakwal na jihar Rivers a ranakun Litinin da Talatan nan, inda alkalin kotun ya bada umarnin a tsare su a cikin jirginsu karkashin gadin sojojin ruwan Najeriya.
Mutanen, wadanda dukkansu suka musanta tuhumar,da ke ana zarginsu da “kokarin satar danyen man fetur a yankin Najeriya ba tare da izini ba kamar yadda VOA HAUSA ta rawai to
Nigeria ta ce jirgin bai riga ya yi lodin mai ba kafin sojojin ruwa su tunkaro shi, sai dai ya shiga wani yanki da aka takaita ba tare da izini ba sannan ya yi yunkurin lodin danyen mai ba bisa ka’ida ba.
Kamfanin man fetur na kasar ya bayyana cewa, satar mai ya kai sama da ganga 400,000 a kowace rana daga man da Najeriya ke hakowa, ya kuma durkusar da kudaden kasar, ya maida kasar dake kan gaba a hakar mai a nahiyar Afirka zuwa ta biyu
