Connect with us

News

Gine-Gine A Kan Layin Wuta Ne Ya Hana Inganta Lantarki A Kano — Minista

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

Ministan Lanrarki na Najeriya, Injiniya Abubakar D. Aliyu, ya ce gine-gine da mutane ke yi a kan hanyar layin wutar lantarki a jihar Kano na kawo cikas ga aikin inganta.

 

Advertisement

Ministan ya bayyana haka ne a yayin ziyarar aiki da ya kai tashoshin rarraba wutar lantarki da gwamnati ta gina a Kumbotso da Rimin Zakara da ke Kano.

 

Advertisement

Tattakin Mutun Miliyon 1: Mun Gaya Masu Tamu Ba Irin Tasu Bace- Amb. Dandago

Injiniya Abubakar ya ce, gwamnati tana son kara yawan karfin wutar lantarki da Kano take samu zuwa megawatt 2,000, amma an kasa yin hakan saboda mutane sun gina gidaje a kan hanyar da babban layin wutar ya bi.

 

Advertisement

Yayin ziyarar, Ministan ya zagaya tashar lantarki ta Dan Agundi tare da Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje, inda ya roki Gwamnan da ya sa baki domin ganin cewar an kawar da gidajen da suka yi kutse a kan layin lantarki daga Kumbotso zuwa Dan Agundi.

 

Advertisement

Ministan lantarkin ya kuma ce babbar tashar lantarki da ke Rimin Zakara za ta bayar da damar kara yawan wutar lantarki da ake samu a jihar Katsina.

 

Advertisement

Sannan ya ce Gwamnatin Tarayya karkashin Shugaba Muhammadu Buhari ta dukufa wajen mayar da Kano wata babbar cibiya ta rarraba wutar lantarki a Arewacin Najeriya.

 

Advertisement

Dangane da haka, ya ce Gwamnatin na gudanar da wani shiri tare da hadin gwiwar kamfanin Siemens na Jamus domin ingantawa da kuma kara yawan wutar lantarki da ’yan Najeriya suke samu a yanzu.

 

Advertisement

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending