News
Gwamnoni sun maida wani martani, bayan Buhari ya zarge su da sace kudaden ƙananan Hukumomi.
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
A daren jiya ne Gwamnonin suka yi wani taro domin domin fitar da kansu daga zargin
A daren jiya ne Gwamnonin suka yi wani taro domin domin fitar da kansu daga zargin shugaban kasa Muhammadu Buhari na wawure kudaden kananan hukumomi.
Idan dai ba a manta ba, Shugaban kasar ya bayyana a wani taro daban-daban cewa gwamnonin sun yi wa kananan hukumomin kasar zagon-kasa, wadanda a lokuta da dama ya zarge su da karkatar da kuɗaɗen su daga asusun tarayya.
Shugaban ya sake nanata zargin ne a jiya a wani taron da aka shirya wa mambobin babbar kwas na 44 (2022) na Cibiyar Nazarin Siyasa da Dabaru ta Kasa, NIPSS, a fadar shugaban kasa, Abuja.
Sai dai gwamnonin da suka mayar da martani game da zargin da shugaban kasar ya yi a jiya, sun ce ba sa cikin masu karkatar da kudaden kananan hukumomi.
Wadanda suka mayar da martani sun hada da gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom; David Umahi na jihar Ebonyi; AbdulRahman AbdulRazaq na Jihar Kwara; Solomon Lalong na jihar Filato; Dapo Abiodun na jihar Ogun da Nyesom Wike na jihar Ribas
Kokarin da aka yi na ganin wasu gwamnonin su mayar da martani a lokacin manema labarai a daren jiya, amma bai haifar da sakamako ba.
Da yake jawabi a wajen taron, shugaba Buhari ya bayar da misali da wani abin da ya faru da wani gwamna da ba a bayyana sunansa ba, domin ya bayyana yadda wasu gwamnonin ke tafka almundahana wajen rabon kayayyakin da aka tanada domin gudanar da aikin kananan hukumomi.
