Connect with us

Sports

Eden Harzard ya ajiye bugawa kasarsa wasa

Published

on

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN 

 

Advertisement

 

Kyaftin din tawagar kungiyar kwallon kafar Belgium Eden Harzard a hukumance ya bayyana murabus din sa daga yiwa kasar sa wasa bayan rashin abin azo a ganin da tawagar ta yi a gasar lashe kofin duniya da ke gudana a Qatar.

Advertisement

 

 

Advertisement

Harzard dai ya kawo karshen shekaru 14 da ya yi ya na bugawa Belgium wasa, ganin yadda ya samu koma baya wajen rawar da ya ke takawa a fagen tamula.

Majalisar Dokokin Peru Ta Tsige Shugaban Kasar

Tun bayan barin gasar Firimiyar Ingila da ya yi zuwa gasar Laliga, ya fara fuskantar naka su a salon wasan sa, kuma ba ta sauya zani ba a wakiltar Belguim da ya yi a gasar lashe kofin duniya.

Advertisement

 

A wani sako da ya wallafa a shafin sa na sada zumunta, ya mika godiyar sa gameda goyon bayan da ya samu a wasannin da ya yiwa kasar.

Advertisement

 

Tawagar ta Belgium dai ta fuskanci babbar koma baya a gasar lashe kofin duniya a wannan karon ta yadda ta gaza fitowa daga matakin rukuni, lamarin da ya sanya mai horas da ita Roberto Martinez aje aikin sa.

Advertisement

 

Hazard ya bugawa kasar ta Belgium wasanni 126 kuma ya ci mata kwallaye 33 tun bayan fara buga mata wasanni a shekarar 2008 ya na dan shekara 17.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending