Sports
Arsenal ta sayi dan wasan Belgium
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Kungiyar Kwallon Kafar Arsenal da ke Ingila ta cimma yarjejeniyar sayen ‘dan wasan gaba na Brighton kuma tauraron Belgium Leandro Trossard akan kudi Fam miliyan 21.
Arsenal ta shiga wannan ciniki ne bayan rasa damar daukar Mykhailo Mudryk ‘dan kasar Ukraine wanda tuni kungiyar Chelsea ta sha gabanta wajen daukarsa.
Rahotanni sun ce, Trossard ya samu matsala da mai horar da kungiyar Brighton Roberto de Zerbi, abin da ya sa shi neman sauya sheka domin ci gaba da gudanar da wasansa.
A wannan kakar wasa, Trossard ya jefa wa Brighton kwallaye 7 da kuma taimaka wa wajen jefa wasu guda 3 daga wasanni 16 da ya buga.
Daga cikin kwallayen da ya ci har da guda 3 da ya zirara a karawar da Brighton ta kara da Liverpool wanda aka tashi 3-3.
Yanzu haka kungiyar Arsenal ke jan ragamar teburin firimiya da maki 47 daga wasanni 18, yayin da Manchester City mai rike da kofin gasar ke matsayi na 2 da maki 39, sai kuma Manchester United wadda ita ma ke da maki 39.
